'Yan Bindiga sun salwantar da rayuka 5 a harin jihar Filato

'Yan Bindiga sun salwantar da rayuka 5 a harin jihar Filato

Duk da ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun salwantar da rayukan mutane biyar na al'ummar Dantako da Nzharuvo dake gundumar Miango ta karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

ASP Terma Tyopev, kakakin hukumar 'yan sanda na jihar shine ya tabbatar da hakan a yayin ganawa a birnin Jos tare da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Najeriya a ranar Juma'ar da ta gabata.

A cewar sa, wannan lamari ya afku ne a daren ranar Alhamis din da ta gabata, da ya raunata mutane da dama tare da asarar dukiya.

Gwamnan jihar Filato; Simon Lalong

Gwamnan jihar Filato; Simon Lalong

Jaridar The Nation ta kawo jerin sunayen wadanda suka riga mu gidan gaskiya a harin kamar haka; Emmanuel Joseph, Christopher Joseph, Peace Joseph, Henry Audu da kuma Samuel Isah.

KARANTA KUMA: Saudiyya za ta ginawa 'yan gudun hijira na Syria masallatai 200 a kasar Jamus

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa, wadanda harin ya raunata ya hadar har da wani karamin yaro dan shekaru hudu da a yanzu suke karbar kulawa a asibitin Enos dake Miango.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, an samu wani Bawan Allah da ya shafe shekaru 37 bai rasa sallar jam'i a masallacin Fiyayyen halitta dake birnin Madinah.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel