Bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyu, shugaba Buhari ya koma fadar sa ta Villa

Bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyu, shugaba Buhari ya koma fadar sa ta Villa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma garin Abuja a yau Juma'a bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai jihar Filato, inda ya halarci sallar Juma'a da daruruwan musulmi a masallacin fadar sa ta Aso Rock dake birnin na tarayya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, wadanda suka halarci sallar ta Juma'a da shugaba Buhari sun hadar da shugaban hukumar NIA; Alhaji Ahmed Rufa'i da kuma shugaban hukumar DSS; Lawal Daura.

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari

A safiyar ranar Juma'ar a jihar ta Filato, shugaba Buhari ya kaddamar da wani sabon shiri na samar da kayan aiki na noman zamani, wanda shine cikon manufa ta kai ziyarar sa jihar.

KARANTA KUMA: Lafiya Jari: Amfani 10 na Dabino ga lafiyar bil Adama

Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito cewa, a yayin ziyarar ta shugaba Buhari ya kuma kaddamar da wani shiri kan zaman lafiya tare da yabawa gwamnan jihar Simon Lalung wajen hada kawunan al'ummar jihar sa.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, masarautar kasar Saudiyya zata ginawa 'yan gudun hijira na Syria masallatai 200 a kasar Jamus da ta basu mafaka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel