Gwamnatin jihar Kano ta alanta Karin albashi ga malaman jihar

Gwamnatin jihar Kano ta alanta Karin albashi ga malaman jihar

A yunkurin karfafa ingancin ilimi a makarantun gwamnati, gwamnatin jihar Kano zata karawa malaman gwamnati albashi da kasha 20 cikin 100.

Shugaban kwamitin sabuwar shirin ilimin jihar, Farfesa Garba Shehu, ya alanta wannan ne a wani hira da ya gabatar da manema labarai a yau Juma’a a garin Zaria.

Ya ce mambobin kwamitin sun zo Zarai ne domin kwaikwayon shirin da aka shirya kafin yanzu.

“An rigaya da gamawa. Zamu bayyanashi cikin shekaran nan. Muna sa ran karashewa saboda ya samu shiga cikin kasafin kudin shekara mai zuwa,” Yace.

Gwamnatin jihar Kano ta alanta Karin albashi ga malaman jihar

Gwamnatin jihar Kano ta alanta Karin albashi ga malaman jihar

Farfesa Shehu yace karkashin wannan sabon shirin, za’a karawa malaman makarantu albashi da akalla kasha 20 cikin 100 na abinda suke karba.

KU KARANTA: Birane 50 mafi hatsari a duniya

Ya kara da cewa bayan Karin albashin ake sa ran za’a fara a 2019, kwamitin na bada shawaran wasu kasu more rayuwa irinsu Karin girma, samar da giddajen ma’aikata, bashin motoci ko mashina, da kuma wasu abubuwan da zai jawo hankulan mutane zuwa koyarwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel