Harin Rann: Hukuma ta fitar da adadin soji, 'yan sanda da su ka mutu

Harin Rann: Hukuma ta fitar da adadin soji, 'yan sanda da su ka mutu

- A yau ne hukumar 'yan sanda a jihar Borno ta fitar da adadin jami'an soji da 'yan sanda da harin Rann ya ritsa da su

- A satin da ya gabata ne mayakan kungiyar Boko Haram su ka kai hari sansanin jami'an tsaro dake Rann, shelkwatar karamar hukumar Kalabalge, a jihar Borno

- Kwamishinan 'yan sanda a jihar Borno ya ce an tura jami'an tsaro 500 a rundunar Ofireshon Lafiya Dole

Hukumar 'yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da cewar dakarun soji 6 da 'yan sanda 4 harin Rann ya ritsa da su.

A satin da ya gabata ne mayakan kungiyar Boko Haram su ka kai wani harin bazata a sansanin jami'an tsaro dake garin Rann, shelkwatar karamar hukumar Kala Balge, a jihar Borno.

Harin Rann: Hukuma ta fitar da adadin soji, 'yan sanda da su ka mutu

Harin Rann: Hukuma ta fitar da adadin soji, 'yan sanda da su ka mutu

Kwamishinan sanda a jihar, Mista Damian Chukwu, ya sanar da hakan yayin amsa tambayoyi a taron 'yan sanda na wata.

"A harin da aka kai na kwanan nan a karamar hukumar Kala Balge, 'yan sanda hudu da sojoji shida ne su ka mutu," inji Chukwu.

DUBA WANNAN: Zargin magudin zaben 2019: Majalisar dattijai ta kafa kwamitin binciken wasu na'urori da aka shigo da su a sace

Kazalika ya sanar da cewar kimanin jami'an tsaro 500 na hukumar 'yan sanda na cikin rundunar Ofireshon Lafiya Dole.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN) ya rawaito cewar, sashen majalisar dinkin duniya mai kula da aiyukan agaji ya ce an kashe jami'an su guda uku tare da jikkata wasu uku tare da bacewar wata ma'aikaciyar lafiya duk a harin na ranar 1 ga watan Maris din da muke ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel