Nigerian news All categories All tags
Tsoho dan shekara 70 yayi wa yarinya 'yar shekara 11 fyade

Tsoho dan shekara 70 yayi wa yarinya 'yar shekara 11 fyade

- Tsoho dan shekara 70 yayi lalata da daliba ‘yar shekara 11 a makarantar da yake gadi

- Matsalar fyade kenan da ta zama ruwan dare a kasar nan, wanda hakan baraza nane ga al'ummar mu musamman ma yara mata

Tsoho dan shekara 70 yayi wa yarinya 'yar shekara 11 fyade

Tsoho dan shekara 70 yayi wa yarinya 'yar shekara 11 fyade

Wani tsoho mai gadi dan shekara 70, mai suna Morounmubo Ayinde, yayi wa wata yarinya ‘yar shekara 11 fyade, yarinyar wadda take ’yar makarantar sakandaren da tsohon yake gadi a birnin Ilorin dake jihar kwara.

DUBA WANNAN: Amurka ta daina sayen danyen man fetur a Najeriya

‘Yan sanda sunyi nasarar kama Ayinde, mai gadin makarantar sakandaren Okelele, a garin Ilori inda ya aikata wannan laifi a karshen makon daya wuce a cikin harabar makarantar.

Ya yaudare ta ne zuwa wane bangaren makarantar inda ya aikata fyaden da ita, bayan tazo neman ruwan sha a hannun sa. Asirin sa ya tonu ne ta hanyar wani mutum da ya ganshi yayi ihu jama’a suka kawo dauki.

An kaishi ma’aikatar Ilimi ta garin Ilori a jiya, inda ya bayyan cewa sharrin shaidan ne ya kaishi ga aikata wannan mummunan aiki. Yace bai taba aikata irin wannan abun ba tunda aka dauke shi gadi daga ma’aikatar Ilimi, wanda ya kai shekara hudu ya na gadin makarantar.

Babbar sakataren garin, Hajia Maryam Ayo Garuba, tace ta saka a kai yarinyar asibiti domin a duba lafiyar ta, sun tabbatar da gaskiyar lamarin, ta kuma yanke shawarar mikashi zuwa ga hukumar ‘Yan sanda domin hukuncin da za ayi masa ya zama darasi ga wasu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel