Nigerian news All categories All tags
Zargin magudin zaben 2019: Majalisar dattijai ta kafa kwamitin binciken wasu na'urori da aka shigo da su a sace

Zargin magudin zaben 2019: Majalisar dattijai ta kafa kwamitin binciken wasu na'urori da aka shigo da su a sace

- Majalisar dattijai ta zargi gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da odar wasu na'urori da niyyar magudin zabe

- Sanata Dino Melaye ya kwarmata zancen a zauren majalisar yayin zamanta na yau

- An kafa wani kwamitin gaggawa domin binciken zargin

Majalisar dattijai ta zargi gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da shigo da wasu na'urori a asirce domin yin magudi a zaben shekarar 2019.

Zargin magudin zaben 2019: Majalisar dattijai ta kafa kwamitin binciken wasu na'urori da aka shigo da su a sace

Dino Melaye

Sanatan Kogi ta yamma, Dino Melaye, ya kwarmata zancen a zauren majalisar yayin zamanta na yau, yana mai bayyana cewar jami'an kwastam sun yi ram da na'urorin domin ko takardun saya ko shigo da su babu.

DUBA WANNAN: Rashin tausayi: Ya sace katin cire kudi na 'yar fansho, ya yiwa asusunta karkaf

Melaye ya bayyana cewar yana isassun shaidu a kan abinda yake fada kuma a yanzu haka mai bawa gwamnan jihar shawarar a kan harkokin tsaro, Kaftin Jerry Omodara (mai ritaya) na ofishin hukumar kwastam domin karbar kayan.

Tuni majalisar ta kwafa wani kwamitin gaggawa domin binciken zargin tare da umartar kwamitin ya gaggauta kawo rahoton sa ga majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel