Madalla! Kamfanoni sumunti zasu rage farashin sumuntin su a Nigeria

Madalla! Kamfanoni sumunti zasu rage farashin sumuntin su a Nigeria

- Kamfanonin suminti zasu rage farashin sa

- Masu ruwa da tsaki na harkar ta suminti sun gana da Osinbajo

- Gwamnati zata taimakawa masu sana'ar ta siminti

Gamayyar kamfunnan suminti da kuma manyan yan kasuwa dillallan sa sun sanar da cewa nan ba da dadewa ba zasu karyar da kudin sumintin a kasuwa.

Madalla! Kamfanoni sumunti zasu rage farashin sumuntin su a Nigeria
Madalla! Kamfanoni sumunti zasu rage farashin sumuntin su a Nigeria

KU KARANTA: Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta

Mun samu labari daga majiyar mu cewa shugaban kamfanin da ke yin sumintin nan na BUA watau Alhaji Abdussamad Isyaka rabi'u shine ya bayyana hakana wata fira da yayi da yan jarida lokaci kadan bayan sun gama ganawa da mukaddashin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.

Legit.ng ta samu labarin cewa Shugaban na kamfanin BUA ta ta'allaka tsadar da sumintin yayi da rashin imani na wasu yan kasauwa sannan kuma da karancin wani muhimmin sinadarin da ake anfanin da shi wajen yin sumintin na LPFO a turance.

A wani labarin kuma, kawo yanzu dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta bayyana mana cewa kawo yanzu baitul malin kasar Najeriya ta kai dalar Amurka biliyan 43.2, yawan da bata taba yi ba tun kimanin shekaru hudu da suka gabata kamar yadda babban bankin Najeriya ya bayyana a jiya Laraba.

Haka ma dai gwamnan babban bankin Najeriya din Mista Godwin Emefiele ya yi hasashen cewa baitul malin kasar zai iya kaiwa dalar Amurka biliyan 60 kafin shekarar 2019 indai har aka cigaba da tafiya yadda ake yanzu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel