Nigerian news All categories All tags
Matsin tattalin arziki: Binciken masana ya bankado wasu bankunan Najeriya dake fuskantar barazanar durkushewa

Matsin tattalin arziki: Binciken masana ya bankado wasu bankunan Najeriya dake fuskantar barazanar durkushewa

Wani sabon jadawali da aka fitar sakamakon bincike da wata cibiyar bincike kan harkokin kudi da kuma tattalin arziki ta Fitch Rating tayi ya bayyana cewa bankuna da dama da suke a matsayi na biyu a kasar nan da kuma ke da kadarorin da suka kasa Naira tiriliyan 2 ka iya durkushewa.

Jadawalin binciken dai ya bayyana cewa bankunan za su iya durkushewa ne idan har darajar kudin Najeriya na Naira suka sake faduwa a kasuwar duniya zuwa Naira 450 duk dalar Amurka.

Matsin tattalin arziki: Binciken masana ya bankado wasu bankunan Najeriya dake fuskantar barazanar durkushewa

Matsin tattalin arziki: Binciken masana ya bankado wasu bankunan Najeriya dake fuskantar barazanar durkushewa

KU KARANTA: Neman a saki Zakzaky: Yan shi'a sun tare titunan garin Abuja

A wani labarin kuma, mun samu cewa hukumar nan dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Economic and Financial Crimes Commission EFCC, a takaice ta kama ma'aikatan duk da suke zargi da satar kudin hukumar jarabawar share fagen shiga Jami'a watau Joint Admissions and Matriculation Board, JAMB.

Cikin wadanda aka kama hadda matar nan da zancen ta ya shahara dake aiki a ofishin JAMB din na jihar Benue dake garin Makurdi mai suna Philomina Chieshe wadda ta ce maciji ne ya hadiye kudaden hukumar har Naira miliyan 36.

Legit.ng ta samu cewa jami'ar Uwar gida Philomina da aka bincike ta dai ta fadawa jami'an hukumar na EFCC cewa kudaden da suka bace shugaban hukumar ne na jihar ke aiken ta ta ciro mashi su inda kuma yake anfani da su wajen aikace-aikacen ofis da kuma na kashin kansa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel