Zaman dar-dar: Kasar Amurka ta gano makarkashiyar kai mata harin nukiliya

Zaman dar-dar: Kasar Amurka ta gano makarkashiyar kai mata harin nukiliya

Fadar mulki ta kasar Amurka da ake kira da Pentagon dake da mazauni a birnin Washington ta ce ta bankado wasu muhimman batutuwan dake nuni da cewa wasu abokan gabar su na shirin kai masu kazamin harin Nukiliya.

Da yake karin haske game da lamarin, mataimakin shugaban jami'an tsaron hadin gwuiwar kasar Janar Paul Selva ya bayyana cewa tabbas wannan tamkar takalar hancin kasar ne kuma ba za su taba bari hakan ta faru ba.

Zaman dar-dar: Kasar Amurka ta gano makarkashiyar kai mata harin nukiliya

Zaman dar-dar: Kasar Amurka ta gano makarkashiyar kai mata harin nukiliya

KU KARANTA: Zakzaky: Yan shi'a sun hargitsa garin Abuja

Legit.ng dai ta samu cewa Janar Paul ya bayyana cewa wannan ne ma ya sa kasar ta Amurka take ta sauya shire-shiren ta ta fuskar tsaron domin maida martani ga dukkan wanda ya nemi ya tabo ta.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa kasar ta Amurka na zaman doya da manja yanzu haka da kasar daular musulunci ta Iran da kuma kasar Koriya ta Arewa.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Birtaniya dake nahiyar Turai ta bayyana fara shirin ta na zuba tsabar kudin da suka kai kusan dala miliyan daya wajen gina sabon bangaren gidan yari a Najeriya.

Wannan dai na kunshe ne a cikin jawabin sakataren harkokin wajen kasar ta Birtaniya Boris Johnson wanda ya kuma ce akwai yarjejeniyar sauyin gidan yari na dole tsakanin kasashen biyu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel