Nigerian news All categories All tags
Obasanjo, ministan Buhari sun isa birnin Maiduguri don kaddamar da shirin korar yunwa

Obasanjo, ministan Buhari sun isa birnin Maiduguri don kaddamar da shirin korar yunwa

Tsohon shugaban kasar Najeriya da ke zaman shugaban kasar na farko a wannan jamhuriyar Cif Olusegun Obasanjo ya isa birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin halartar taron masu ruwa da tsaki da ke da zummar korar yunwa daga Najeriya karo na uku.

Mun samu dai cewa tsohon shugaban kasar ya hadu da ministan ayyukan gona na gwamnatin Buhari Cif Audu Ogbe da ma sauran gwamnonin shiyyar ta Arewa maso gabas domin tabbatar da samun nasarar shirin.

Obasanjo, ministan Buhari sun isa birnin Maiduguri don kaddamar da shirin korar yunwa

Obasanjo, ministan Buhari sun isa birnin Maiduguri don kaddamar da shirin korar yunwa

KU KARANTA: Baitulmalin Najeriya tayi cikar da bata taba yi ba tun mulkin Jonathan

Legit.ng ta samu kuma cewa tsohon shugaban kasar ya samu kyakkyawar tarba daga gwamnan jihar ta Borno Kashi Shettima a filin sauka da tashi na jiragen jihar da ranar yau.

A wani labarin kuma, Kawo yanzu dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta bayyana mana cewa kawo yanzu baitul malin kasar Najeriya ta kai dalar Amurka biliyan 43.2, yawan da bata taba yi ba tun kimanin shekaru hudu da suka gabata kamar yadda babban bankin Najeriya ya bayyana a jiya Laraba.

Haka ma dai gwamnan babban bankin Najeriya din Mista Godwin Emefiele ya yi hasashen cewa baitul malin kasar zai iya kaiwa dalar Amurka biliyan 60 kafin shekarar 2019 indai har aka cigaba da tafiya yadda ake yanzu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel