Rashin tausayi: Ya sace katin cire kudi na 'yar fansho, ya yiwa asusunta karkaf

Rashin tausayi: Ya sace katin cire kudi na 'yar fansho, ya yiwa asusunta karkaf

- An gurfanar da wani matashi, Obinna Otigba, mai shekaru 30 bisa tuhumar sa da cire miliyan N2m daga asusun wata makwabciyar sa

- Otigba ya cire dukkan kudin ne bayan ya sace katuna biyu da matar ke amfani da su wajen cire kudi

- Kotu ta bayar da shi beli a kan N500,000 bayan ya ki amsa laifin da ake tuhumar sa da shi

Wani matashi Obinna Otigba mai shekaru 30 a duniya ya gurfana gaban kotun majistare ta O.J. Awope bisa tuhumar sa da cire kudin wata makwabciyar su har miliyan N2m.

An gurfanar da shi yau, Alhamis, a wata kotun majistare dake Ikeja a garin Legas bisa tuhumar sa da laifukan sata da halin hankaka; mayar da dan wani naka.

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Ezekiel Ayirinde, ya ce wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a tsakanin ranar 17 zuwa ranar 28 na watan Nuwamba, 2017.

Rashin tausayi: Ya sace katin cire kudi na 'yar fansho, ya yiwa asusunta karkaf

Ya sace katin cire kudi na 'yar fansho, ya yiwa asusunta karkaf

"Wanda ake tuhumar ya sace katin cire kudi (ATM) guda biyu na wata mata da su ke zaune gida sannan ya gudu kuma ya cigaba da cire kudi daga asusun matar da ta tara kudinta na barin aiki har saida ya yiwa asusun karkaf," inji Ayorinde.

DUBA WANNAN: Illolin ranto kudi daga China: Amurka ta gargadi Najeriya, kasashen Afrika

Alkalin kotun ya bayar da belinsa a kan kudi N500,000 tare da gabatar da shaidu guda biyu masu aiki da gwamnatin jihar Legas kuma su kasance su na da cikakkun takardun biyan haraji.

An daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Maris bayan wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel