Nigerian news All categories All tags
Bola Tinubu ya kasa shawo kan rikicin da ya dabaibaye Jam'iyyar APC

Bola Tinubu ya kasa shawo kan rikicin da ya dabaibaye Jam'iyyar APC

- Har yanzu dai rikicin cikin APC ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya

- Yunkurin Bola Tinubu ba ya cin ma ruwa sai dai ma akasin haka

- Kan Jam’iyyar mulki ya rabu biyu ne tsakanin Tinubu da Oyegun

Bayan nada Bola Tinubu sasanta kan Jam'iyya ne Majalisar Jam’iyyar ta APC ta kara wa’adin Shugaban ta Cif John Oyegun. Bola Tinubu da sauran mutanen sa sun soki wannan abu inda su kace ya sabawa ka’idar Jam’iyya da dokar kasar.

Bola Tinubu ya kasa shawo kan rikicin da ya dabaibaye Jam'iyyar APC

An nada Bola Tinubu ya sasanta rikicin Jam’iyyar APC mulki

Kafin nan kuwa dama Bola Tinubu ya kai kuka wajen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a wasika inda yace Shugaban Jam’iyyar na kasa John Oyegun na kokarin hana sa aikin da aka nada sa ya kuma lafta wasu zargi a kan sa.

KU KARANTA: Fastocin takarar Shugaban kasa na Dino Melaye sun fara yawo a gari

Shi kuwa wani tsohon Sojan kasar Kanal Tony Nyiam yace tun farko Shugaba Buhari ya raba kan Jam’iyyar da ya nemi Bola Tinubu wanda yake waje da ya dinke barakar cikin gida. Nyiam yana ganin an shiga cikin hurumin Jam’iyya.

Bola Tinubu wanda Jigo ne a Jam’iyyar ya dai soma aikin da aka nada shi sai dai har yanzu akwai cikas. Kwanaki mu ka ji cewa ma Jigon Jam’iyyar yayi kokarin shawo karshen rikicin Ganduje da Kwankwaso amma abin sam bai yiwu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel