Nigerian news All categories All tags
An damke wani Kare da laifin kisan Jaririya kwanaki 8 da haihuwar ta

An damke wani Kare da laifin kisan Jaririya kwanaki 8 da haihuwar ta

Wata hukumar kula da dabbobi wato Lee County Animal Control, ta tsare wani Kare da laifin kekketa wata jaririya har Lahira bayan kwanaki takwas da haihuwar ta a birnin Virginia na kasar Amurka.

Wani babban jami'i na hukumar, Gary Parsons ya bayyana cewa, wannan Kare dai ruwa biyu ne kuma akwai yiwuwar za a zartar ma sa da hukuncin kisa a wasu lokuta na gaba da zarar an kammala bincike.

An damke wani Kare da laifin kisa

An damke wani Kare da laifin kisa

A yayin da hukumar take ci gaba da tsare wannan Kare, jaridar The Punch ta ruwaito cewa ya raunata jaririyar da a karshe tace ga garinku nan a cibiyar lafiya ta Knoxville Medical Center.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi ta kai komo da wannan jaririya har asibitoci uku kafin ajali ya katse ma ta hanzari.

KARANTA KUMA: Kiwon Lafiya: Amfanin Gishiri ga Lafiyar Dan Adam

Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar PDP ta budewa shugaba Buhari aiki dangane da furucinsa na kasar Ghana a yayin ziyara kwanaki biyu da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel