Babu Najeriya babu maganar karayar tattalin arziki - IMF

Babu Najeriya babu maganar karayar tattalin arziki - IMF

- Najeriya ta fita daga matsin da ta shiga na durkushewar tattali

- An nemi a tsawwala haraji kuma a rage maida hankali kan fetur

- Zai yi wahala a kara farashi a Najeriya duk da kiran da IMF tayi

Mun samu labari cewa Hukumar da ke bada lamuna na Duniya watau IMF ta bayyana cewa ba shakka Najeriya ta fita daga matsin lambar da ta samu kan ta a baya na matsin tattalin arziki sai dai IMF tace har yanzu akwai sauran aiki.

Babu Najeriya babu maganar karayar tattalin arziki - IMF

Har yanzu sai Najeriya ta dage wajen rabuwa da fetur

A baya dai tattalin arzikin Najeriya ya durkushe sai dai yanzu abubuwa sun dawo daidai. IMF ta fitar da wannan jawabi a Birnin Washington na Amurka a jiya Laraba. Duk da haka dai Hukumar tace sai an bi a sannu kar a koma gidan jiya.

KU KARANTA: Ana neman karbe kujerar Shugaban Majalisar Dattawa

IMF ta yabawa sabon tsarin bunkasa tattalin arzikin da Gwamnatin Shugaba Buhari ta kawo na ERPG inda kuma ta yabawa manufofin babban bankin Najeriya na CBN na tsaida farashin Dala. Yanzu haka dai Dalar Amurka ta na kan N360.

Bayan nan Hukumar ta nemi a kawo gyara a wajen sha’anin haraji a kasar wanda zai taimakawa Gwamnati. An kuma yabawa kokarin wannan Gwamnati na gyara farashin fetur da sauran su sai dai an nemi a duba lamarin Jihohi da kananan Hukumomi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel