Mutane 13 ne da Buhari ya turo bamu amince da su ba tun farkon wannan gwamnatin - Saraki

Mutane 13 ne da Buhari ya turo bamu amince da su ba tun farkon wannan gwamnatin - Saraki

- Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya ce mutane 13 kacal majalisa ta ki yarda da nadinsu a mukaman gwamnati

- Saraki ya ce tun bayan hawan shugaba Buhari kujerar mulki, ya turo mutane 240 da ya ke bukatar sahalewar majalisar kafin ya nada su mukami

- Saraki na wadannan kalamai ne a jiya yayin tantance Ibrahim Rufai Imam a matsayin Grand Khadi na kotun daukaka kara dake Abuja

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya ce majalisar ta ki yarda da mutane 13 ne kacal daga cikin mutane 240 da Buhari ya aiko ma ta domin tantancewa.

Saraki na wadannan kalamai ne yayin tantance Ibrahim Rufai Imam a matsayin babban alkalin kotun daukaka kara ta shari'a dake Abuja.

Ya kara da cewar majalisar ta fara aiki ne tun watan Yuni na shekarar 2015 kuma shugaba Buhari ya aiko mutane 240 domin tantancewa.

Mutane 13 ne da Buhari ya turo bamu amince da su ba tun farkon wannan gwamnatin - Saraki

Bukola Saraki

"A madadin dukkan 'yan majalisar dattijai, ina taya sabon Grand Khadi na kotun shari'a, Ibrahim Rufai Imam, murna tare da yi masa fatan gama wa'adin shugabancinsa lafiya. Ina ma Ka fatan kammala yin aikin ka cikin nasara," inji Saraki.

DUBA WANNAN: Ya biya miliyan N1m domin a sace 'yar mutumin da nake bi bashin kudi

Sannan ya ciga da cewa, "majalisa na da rawar da zata taka da ta wuce kawai amsa dukkan abinda ya biyo ta gabanta. Wannnan tantancewa ta yau ta nuna irin hadin kai da goyon baya da mu ke bawa bangaren zartarwa."

Majalisar ta tabbatar da nadin Imam ne bayan gansuwa da rahoton kwamitinta na bangaren shari'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel