Nigerian news All categories All tags
Kashi 20% daga cikin yaran dake kammala makarantar firamare a Najeriya ke iya karatu - Bankin duniya

Kashi 20% daga cikin yaran dake kammala makarantar firamare a Najeriya ke iya karatu - Bankin duniya

- Bankin Duniya ta ce kashi 20% daga cikin daliban Najeriya da suka kammala makarantar firamare ne suka iya karatu

- Bankin Duniya ta ce kananan yara basa samun ilimin da ya kamata

Wata sabuwar rahoto da Bankin Duniya ta fitar a ranar Talata ta ce, kashi 20% daga cikin yaran Najeriya ke iya karatu bayan sun kammala makarantar firamare.

Bankin ta bayyana haka ne lokacin taron cigaban al’umma da harkan ilimi na shekara 2018 da Bankin duniya da hadin gwiwar Ma’aikatar Ilimi da Ma’aikatar harkan kudi na Najeriya suka kaddamar a birnin Abuja a ranar Talata.

Kashi 20% daga cikin yaran dake kammala makarantar firamare a Najeriya ke iya karatu - Bankin duniya

Kashi 20% daga cikin yaran dake kammala makarantar firamare a Najeriya ke iya karatu - Bankin duniya

Rahoton ya nuna miliyoyin kanan yara a kasashen da basu da arziki basa samun rayuwa mai kyau a lokacin da suka girma, saboda rashin samun ingantaccen ilimin makarantar Frimare da na Sakandare.

KU KARANTA : Fiye da 'yan sanda 2,000 aka tura jihar Filato saboda ziyarar da Buhari zai kai jihar

Rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa idan aka gaza daukan matakan da za su inganta ilimi a kasashen da basu da arziki, rashin cigaba da talauci zai yiwa al’ummar kasashen yawa.

Wasu manyan jami’an bankin duniya, Deon Filmer da Halsey Rogers, sun cce, al’amarin Najeriya yana da matukar ta da hankali, saboda kanana yara basa samun ilimin da yakamata, amma idan aka dauki mataki mai kyau al’amarin zai gyaru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel