Nigerian news All categories All tags
EFCC ta sake gurfanar da tsohon sakataren INEC bisa laifin karbar cin hanci daga Diezani

EFCC ta sake gurfanar da tsohon sakataren INEC bisa laifin karbar cin hanci daga Diezani

Hukumar hana cin hanci da rashawa wato (EFCC) a ranar Laraba ta sake gurfanar da tsohon Sakataren hukumar zabe ta (INEC), Mr. Christian Nwosu, bisa ga laifin karbar kudi daga hannun tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Alison-Madueke.

Ya gurfana ne tare da Tijjani Bashir da Alison Madueke wadda har yanzu ba’a san inda take ba, sai Yisa Adedoyin, wadda ta amsa laifinta tun kwanakin baya na karbar cin hancin N30m daga hannun Alison-Madueke don magudin zabe na shekarar 2015, wadda daga baya tace kuma bata amsa laifin aikata hakan ba.

EFCC ta sake gurfanar da tsohon sakataren INEC bisa laifin karbar cin hanci daga Diezani

EFCC ta sake gurfanar da tsohon sakataren INEC bisa laifin karbar cin hanci daga Diezani

KU KARANTA: Dubi hotunan 'yan fashi da makami 48 da aka kama tare da makamai a Jihar Neja

Laifuffukan an aikata su ne a ranar 27 ga watan Maris, da kuma ranar 7 ga watan Afirilun 2015. Hukumar yaki cin hancin ta ja akalar binciken ta bayan da ta gama bayyana shaidun ta a gaban shari’a. Mai gabatar da kara, Rotimi Oyedepo yace bazai kara gabatar da wata shaida ba duk da duk da gyaran da akayi a karar.

Alkali mai yanke hukunci Mohammed Idris yace hukumar na da damar yin gyara bisa ga tuhumar da takeyi kafin a lokacin yanke hukunci. Doka tace ko wane lokaci kafin a yanke hukunci, duk da bata bayyana lokaci ba, amma na yarda da gyara a cikin karar da akeyi, in ji Alkalin.

Bayan sake gurfanar ta su ya bar wadan da ake tuhumar a kan beli da aka badasu tun a waccan shari’ar ta farkon da aka badasu. Alkalin ya kuma dage sauraren karar zuwa 29 ga watan Maris, inda yake bukatar a kawo masa bayanai a rubuce a kan wadan da ake tuhuma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel