Nigerian news All categories All tags
PDP ga Buhari: Ka yi koyi da shugaban kasar Ghana, ka daina kunyata Najeriya

PDP ga Buhari: Ka yi koyi da shugaban kasar Ghana, ka daina kunyata Najeriya

Jam'iyyar adawa ta PDP, ta kirayi shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan ya yi amfani da ziyarar kasar Ghana wajen daukan darussa daga takwaransa na kasar, Nana Akufo-Addo, dangane da yadda za a gudanar da zaman lafiya, hadin kai da kuma habakar tattalin arziki a Najeriya.

Jam'iyyar ta soki shugaba Buhari na cewar zai bayar da taimako ga kasar Ghana wajen yakar cin hanci da rashawa, bayan rashawa ta mamaye kasar sa kamar yadda kididdigar bincike ta duniya ta fitar wajen haskaka yadda Najeriya ta tabarbare a karkashin gwamnatin sa.

Shugaba Buhari tare da shugaban kasar Ghana

Shugaba Buhari tare da shugaban kasar Ghana

Kakakin jam'iyyar na kasa Kola Ologbondiyan, shine ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata da cewa, ya kamata a ce kunya ta rufe shugaba Buhari da makarraban sa a yayin da shugaban kasar Ghana ya samu lambar yabo akan tattalin arziki da zaman lafiya mai inganci a kasar sa.

KARANTA KUMA: Kiwon Lafiya: Amfanin Gishiri ga Lafiyar Dan Adam

Yake cewa, Najeriya karkashin gwamnatin shugaba Buhari ta shiga cikin tasku na matsin tattalin arziki baya ga tashin-tashina da zubar da jini dake ci gaba da kaiwa wani munzali a fadin kasar nan.

Jam'iyyar ta nemi shugaba Buhari akan yayi koyi da shugaba Akufo-Addo dangane da irin rawar da ya taka a shekarar farko ta shugabancin kasar Ghana.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne hukumar 'yan sanda ta cafke wasu barayin shanu 10 a jihar Benuwe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel