Nigerian news All categories All tags
Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta kai karar Oyegun wajen Buhari

Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta kai karar Oyegun wajen Buhari

- Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta yi fatali da karin lokacin da aka yiwa Oyegun

- APC jihar Legas ta ce karawa Oyegun wa'adin shekara daya a kujerar shugaban jam'iyyar APC ya sabawa tanade tanade kundin tsarin mulkin jam’iyyar

Bayan fatali da karin lokaci da aka yiwa shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Cif John Odigie Oyegun, jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta kai karar, Cif Oyegun, wajen shugaban kasa, Muhammadu Buhari, akan al’amarin.

Jagoran jam’iyyar APC na jihar Legas, Cif Tajudeen Olusi, ya bayyana haka ne a ranar Laraba.

Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta kai karar Oyegun wajen Buhari

Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta kai karar Oyegun wajen Buhari

Cif Tajudeen Olusi, ya ce jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne bayan sun tattauna da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC reshen jihar Legas.

KU KARANTA : Rikicin kasuwan magani: Gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da mutane 63 a kotu

Cif Olusi, ya ce APC jihar Legas a ashirye ta ke ta bayyana wa shugba Buhari, bacin ran ta akan kara wa, Cif John Oyegun, wa’adin shekara daya a kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Olusi wanda ya soki wannan kudiri ya ce, karawa Shugaban jam’iyya lokaci abu ne da ya sabawa tanade tanade kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel