Nigerian news All categories All tags
Fiye da 'yan sanda 2,000 aka tura jihar Filato saboda ziyarar da Buhari zai kai jihar

Fiye da 'yan sanda 2,000 aka tura jihar Filato saboda ziyarar da Buhari zai kai jihar

- Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Filato a ranar Alhamis

- Gwamann jihar Nasarawa Tanko Almakura ya isa filin jirgin saman jihar Filato dan jiran isowar Buari

Rundunar ‘yansanda jihar Filato ta ajiye jami’an ‘yansanda 2,435 dan samar da tsaro a lokacin ziyarar kwana biyu da shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kai jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Filato, Mista Terna Tyopev, bayyana haka a lokacin da ya zanta da manema labaru a ranar Alhamis.

Fiye da 'yan sanda 2,000 aka tura jihar Filato saboda ziyarar da Buhari zai kai jihar

Fiye da 'yan sanda 2,000 aka tura jihar Filato saboda ziyarar da Buhari zai kai jihar

Mista Terna Tyopev, yace rundunar ‘yansandan jihar Filato ta ajiye jami’an yansanda 2,435 saboda kare rayuka da dukiyoyin mutanen jihar yayin da Buhari zai ziyarci jihar.

KU KARANTA : Hukumar lekan asiri ta NIA suna farautar wani Jakadan Najeriya

Yanzu haka gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Tanko Almakura, ya isa filin jirgin sama na jihar Filato dake Barikin Ladi dan jiran isowar shugaba Buhari.

Jihar Filato tana cikin jihohin shida da hadimin shugaban kasa a fannin watsa labaru, Femi Addesina, ya ce shugaba Buhari zai ziyar ce su a ranar Litinin

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel