Nigerian news All categories All tags
Kisan Bilyaminu: Ainihin dalilin da ya sa kotu ta bada belin Maryan Sanda

Kisan Bilyaminu: Ainihin dalilin da ya sa kotu ta bada belin Maryan Sanda

Wata babban kotu da ke zaune a Abuja a jiyar Laraba, ta bada belin Maryam Sanda wacce ke garkame a kurkuku da laifin kisan mijinta, Bilyamin Bello, wanda dan tsohon shugaba jam’iyyar PDP ne.

Jastis Yusuf Halilu wanda ya ki bada beli a baya ya bayyana cewa akwai wani dalili kwakkwara da ya gamsar da shi kuma ya sa ya bada belin.

Alkalin ya ce rahoton asibiti ya nuna cewa Maryam na cikin wani mugun hali da jami’an fursunonin ba zasu iya kula da ita ba.

Justis Halilu ya kara da cewa ya gamsu ne saboda banda cewa tanada juna biyu, tana fama da ciwon Asthma.

Kisan Bilyaminu: Ainihin dalilin da ya sa kotu ta bada belin Maryan Sanda

Kisan Bilyaminu: Ainihin dalilin da ya sa kotu ta bada belin Maryan Sanda

Kana lauyoyin gwamnati sun gaza karyata cewa kayayyakin kiwon lafiyan da ke fursunonin ba zai taimakawa wajen kula da Maryan Sanda ba.

KU KARANTA: Hukumar lekan asiri ta NIA suna farautar wani Jakadan Najeriya

Daga karshe, kotu ta bata beli kuma kaidar belin shine mutane 2 su tsaya mata da kuma wani dukiya a Abuja. Kuma an dakatad da karar zuwa ranan 19 ga watan Maris.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel