Nigerian news All categories All tags
Karin wa’adi na jagorancin Oyegun ba kan ka’ida yake ba - Tinubu

Karin wa’adi na jagorancin Oyegun ba kan ka’ida yake ba - Tinubu

- Shugaban jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana karin wa'adin da akayi wa shugaban kwamitin ayyuka, John Odigie-Oyegun ya sabawa dokar jam'iyya

- Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin mai bawa Tinubu shawara ta fannin sadarwa, Tunde Rahman

- Rahman ya ce bashi da masaniya ko an shawarci Tinubu kafin daukar matakin amma ya ce babu yadda za'ayi maigidan na sa ya goyi bayan abinda ya sabawa doka

A ranar Laraba, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Shugaban jami’iyar APC, ya ce karin shekara daya da akayi ma shugaban kwamitin ayyuka, John Odigie-Oyegun, wanda shugabannin kula da al’amurra na jam’iyya suka yi ma shi ya saba ma dokar kasa da ta jam’iyya.

Karin wa’adi na jagorancin Oyegun ba kan ka’ida yake ba - Tinubu

Karin wa’adi na jagorancin Oyegun ba kan ka’ida yake ba - Tinubu

Tunde Rahman, mai ba Tinubu shawara ta fannin sadarwa, ya ce Tinubu ba ya goyon bayan wannan karin lokaci da akayi, ya dai shawarce su da sake tsayawa takara idan wa’adinsu ya yi akan wanna matsayi. Ya kara da cewa APC ya kamata su ringa yin abun da ya dace don shine ya bambanta jam’iyar ta su da sauran.

KU KARANTA: An kafa dokar hana fita a Mambilla bayan wani sabon rikici ya barke

Rahman, ya ce na san uban gidan nawa ya na yin abunda ya san doka ta amince da shi, amma ban sani ba ko sun nemeshi kafin yanke wannan hukunci na kara ma shugaban lokaci bayan cikar wa’adin sa. Sashe na 223 na dokar kasa na shekarar 1999 ta yi maganar zaben shugabannin jam’iyyun siyasa lokaci zuwa lokaci.

Shugaban jam’iyya na Jihar, Cif Henry Ajomale, a ranar 27 ga watan Fabrairu ya halarci taron kungiya a birnin Tarayya in da aka yanke hukunci kan kara ma jagorancin Oyegun, wa’adin shekara daya. Olusi yace, duk da shugaban na su ya halarci taron da aka yi karin wa’adin hakan bazai kawo baraka a jam’iyyar APC ta jihar Legas ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel