Kasar Iceland tana kokarin saka dokar hana yi wa maza shayi

Kasar Iceland tana kokarin saka dokar hana yi wa maza shayi

- Malaman addini sun nuna rashin goyon bayansu bisa dokar da ake kokarin sakawa a kasar Iceland

- Gwamnatin kasar Iceland tana son hana yi wa maza shayi a kasar

- Zata yanke wa duk wanda ta kama yayi ma wani shayi hukuncin shekara shida a gidan yari

Kasar Iceland tana kokarin saka dokar hana yi wa maza shayi

Kasar Iceland tana kokarin saka dokar hana yi wa maza shayi

Shugabannin addini sun nuna bacin rai bisa ga dokar da ake kokarin kafawa ta hana yi wa maza shayi, inda gwamnatin kasar ta yanke cewa duk wanda ta kama yayi wa wani shayi hukuncinsa shine daurin shekara shida a gidan yari.

DUBA WANNAN: Wata sabuwar kungiya ta fito domin sharewa Almajirai hawaye a jihar Kaduna

Salman Tamimi shugaban Kungiyar Musulmai na kasar Iceland, ya kwatanta wannan yunkuri na kafa wannan doka a matsayin hari ga addini. Yi wa mata shayi dama wannan an haramta shi tun shekarar 2005, amma ba wata doka data hana yi wa maza.

Dokar na nuna cewa yi wa maza shayin shiga hakkin yara maza ne, dokar na nuni da cewa inda kadai aka yarda da ayi wa maza shayi shine idan ta kama ta bangaren nema lafiya. Kasar tace zata barwa yaran zabi ne idan sun girma su yi wa kansu ko su bari.

Tamimi ya nuna rashin tunani a kan dokar na maida yin shayi ta’addanci. Duk dai cewar ana ta muhawara a kan takaddamar da dokar wanda shine hanya mafi dacewa a dimokuradiya.

Mista Gunnarsdottir, yace wannan abu ne mai wahala da kuma rudani.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel