An kafa dokar hana fita a Mambilla bayan wani sabon rikici ya barke

An kafa dokar hana fita a Mambilla bayan wani sabon rikici ya barke

- Sabon rikiciya barke a Tsibirin Mambilla kwana daya bayan ziyarar da shugaba Buhari ya kai Jihar

- Gwamnatin Jihar ta kafa dokar hana fita don kwantar da rikicin da kuma bawa jami'an tsaro damar gudanar da ayyukan su

An san ya dokar hana fita a wasu bangarori na jihar Taraba, in da wata sabuwar rikici ta balle tsakanin yan kungiyar yan daba na Mambilla da matasan fulani a yankin.

Abun ya faru ne kafin sa’o’i 24 bayan ziyarar da shugaba Buhari ya kai a jihar. Buhari ya sadu da yan siyasa, da sarakunan garin don a san yanda za’ayi a magance matsalar kuma a samu zaman lafiya a jihar.

Sabon rikici ya barke a Mabilla, an kafa dokar takaita fita

Sabon rikici ya barke a Mabilla, an kafa dokar takaita fita

Gwamnatin Jihar ta sanya dokar ne a garin Mayo Ndaga a kauyen Sardauna a Jihar. An gudanar da taro na tsaro a Gembu wanda kwamandan Soji na 20 bataliya da Kwamandan ‘Yan Sanda, da Hakimin Mambilla da kuma shuwagabannin Fulani duk sun halarta.

KU KARANTA: Tsohon najadu: An kama dan shekaru 63 dake garkuwa da mutane, an samu motocci 35 tare da shi

Majiyar Legit.ng ta gano cewa an dauki matakin baza jami'an tsaro a duk wuraren da rigingimun suka barke don kwantar da tarzoma da kuma zakulo wanda suke da hannu cikin ruruta rikicin don hukunta su.

Wani mazaunin garin Gembu, Alhaji Ibrahim Musa, ya shaidawa manema labarai cewa tsibirin Mambilla wuri ne da mutanen kasar nan dayawa ke fatan zuwa, amma saboda wannan tashe-tashen hankulan ba mai ra’ayin zuwa yanzu.

Ya shawarci Dattawan garin da fadawa Jama’arsu cewa su zauna da juna, in kuwa suka kiya mutane zasu goji zuwa yankin nasu gaba daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel