Nigerian news All categories All tags
Hukumar 'yan sanda ta cafke barayin shanu 10 a jihar Benuwe

Hukumar 'yan sanda ta cafke barayin shanu 10 a jihar Benuwe

Hukumar 'yan sanda ta Benuwe, ta cika hannun ta da barayin shanu goma a karamar hukumar Guma ta jihar.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Fatai Owoseni, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a birnin Makurdi, inda yace barayin 10 sun shiga hannu sakamakon rahotannin wasu makiyaya na garin Guma da sace-sacen shanu yake ci musu tuwo a kwarya.

Owoseni ya bayyana cewa, hukumar ta 'yan sanda za ta ci gaba hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kawo karshen ta'addanci a yankunan jihar.

Jami'an 'yan sanda

Jami'an 'yan sanda

Kwamishinan ya kara da cewa, a halin yanzu hukumar ta cafke miyagu 44 a sassa daban-daban da suke yiwa dokar hana kiwo karan tsaye a jihar.

KARANTA KUMA: Yajin Aiki ya janyo rabuwar kawunan Ma'aikata a Jami'ar Ahmadu Bello

Tuni dai an gurfanar da wannan 'yan ta'adda a gaban kuliya domin zartar musu da hukuncin da ya dace da su kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Talatar da gabata ne hukumar Sojin kasa ta kaddamar da wani sabon barikin soji a jihar Bayelsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel