Nigerian news All categories All tags
Shugabannin arewa sun yi watsi da maganar takarar Buhari, sun bayyana wanda zasu goyawa baya

Shugabannin arewa sun yi watsi da maganar takarar Buhari, sun bayyana wanda zasu goyawa baya

- A jiya ne 'yan siyasar arewa su ka gudanar da wani muhimmin taro a Abuja, birnin tarayya

- Sun yi alla-wadai ta yawaitar tashe-tashen hankula da yawaitar hare-hare a wasu jihohin arewa

- Sun bayyana rashin amincewar su da zabin shugaba Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa da wasu shugabannin arewa su ka yi

A jiya ne manyan 'yan siyasar arewa su ka gudanar da wani taro a Abuja inda su ka tattauna muhimman batutuwan da su ka shafi arewa ta fuskar tsaro da kuma siyasa.

An gudanar da taron ne karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Alhaji Tanko Yakasai, kuma ya samu halartar masu fada a ji daga fadin jihohin arewacin Najeriya.

Shugabannin arewa sun yi watsi da maganar takarar Buhari, sun bayyana wanda zasu goyawa baya

Taron 'yan siyasar arewa da aka yi jiya a Abuja

Yayin taron, an kafa wani kwamiti da zai zakulo hanyoyin da zasu kawo karshen aiyukan ta'addanci da rigingimu masu alaka da kabilanci a arewacin Najeriya, kwamitin zai mika rahotonsa ranar 31 ga watan Maris.

KU KARANTA: An kafa dokar hana fita a Mambilla bayan wani sabon rikici ya barke

A dangane da batun ayyana shugaba Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa da wasu jagororin jam'iyyar APC su ka yi, Yakasai, ya ce ba sa tare da wadannan 'yan siyasa tare da bayyana cewar hakan ya ci karo da tsarin dimokradiyya.

Yakasai ya kara da cewar za su goyi bayan dan takarar da zai samu karbuwa ne kuma su ke da yakinin zai iya kawo canji dangane da yadda abubuwa ke tafiya yanzu.

Kazalika, Yakasai, ya bayyana shakku a kan yiwuwar gudanar da zabe na gaskiya ba tare da magudi a zaben shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel