Nigerian news All categories All tags
Jami’an kwastam sun kama wani mutumi dauke da sama da Miliyan 100 a Kano

Jami’an kwastam sun kama wani mutumi dauke da sama da Miliyan 100 a Kano

- Wani mutumi da ke dauke da makudan Daloli ya shiga hannun EFCC

- An kama wannan mutumi ne a babban filin jirgin Kano zai bar Najeriya

- Rike irin wannan makudan kudi dai a hannu ya sabawa dokar kasar nan

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon kasa watau EFCC tayi nasarar damke wani mutumi dauke da makudan Dalolin kudi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Hukumar EFCC ta kara yin ram da wasu makudan Daloli a filin jirgi

An kama wannan Bawan Allah rike da Daloli a filin jirgi

Yanzu haka an soma binciken wannan batu inda aka kama wannan Bawan Allah mai suna Adamu Rabi’u Mohammed dauke da Dala 370, 000. Mohammed na kokarin hawa jirgin Ethiopia domin ya lula zuwa kasar UAE ta Larabawa.

KU KARANTA: Kamfanin Coca-cola zai karya tarihin shekaru 130 a Duniya

Jami’an Kwastam ne dai su kayi ram da wannan mutumi kamar yadda mu ka samu labari. Yanzu haka dai an mika shi hannun Hukumar EFCC kuma za a maka shi Kotu domin a fara shari’a ba tare da wani bata lokaci ba inji Hukumar.

Dokar kasar dai ta haramta a rika yawo da tsabar kudin da ya haura Dala 10, 000. Kudin da aka kama wannan mutumi da shi sun haura Naira Miliyan 130. Wilson Uwujaren wanda ke magana da yawun EFCC ya bayyana mana wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel