Nigerian news All categories All tags
An jikkata sama da mutane 20 a wani gumurzu da aka fafata tsakanin dalibai da yan Acaba

An jikkata sama da mutane 20 a wani gumurzu da aka fafata tsakanin dalibai da yan Acaba

Kimanin mutane 20 ne suka samu munanan raunuka a sakamakon rikici da ya barke tsakanin daliban sabuwar jami’ar tarayya dake garon Oye Ekiti, FOUYE a jihar Ekiti, inji rahoton rediyo muryar Amurka.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan rikici ya faru ne a ranar Laraba 7 ga watan Maris, kuma daga cikin wadanda suka jikkata akwai wasu yan gari da ba dalibai ba amma suka kutsa kai cikin rikicin.

KU KARANTA: Shari’a saɓanin hankali: Alkalin Kotu ya yanke ma wani ƙaramin Yaro hukuncin shara

Shaidun gani da ido sun bayyana ma majiyar Legit.ng cewa matsalar ta samo asali ne kan biyan dan Acaban kudinsa da wani dalibi zai yi, inda suka shiga cacar baki suna zagin juna har dan Acabar ya sharara ma dalibin mari.

An jikkata sama da mutane 20 a wani gumurzu da aka fafata tsakanin dalibai da yan Acaba

Yan Acaba

“Dan Acaban ne ya fara zabga ma dalibin mari, daga nan sai kawai suka cure, jin hakan ya sanya wasu dalibai da suka hange su suka shiga fadan don taimaka ma dan uwansu, daga nan su ma yan Acaban suka kirawo abokan aikinsu don taimaka ma nasu, hakan ne ya kara ruruta fadan.” Inji shaidan.

Kaakakin jami’ar, Mista Godfrey Bagaji ya tabbatar da faruwar rikicin tsakanin daliban jami’ar da yan Acabar garin, inda ya bayyana cewa basu taba tsammanin hakan zai iya faruwa ba duba da kyakkyawar alakar da jami’ar ke da shi da yan Acaban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel