Nigerian news All categories All tags
Dan takarar PDP ya soki kasafin kudin Jihar Oyo na 2018

Dan takarar PDP ya soki kasafin kudin Jihar Oyo na 2018

- ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Oyo yayi tir da Gwamnatin Abiola Ajimobi

- Seyi Makinde yace akwai matsala a kasafin kudin Jihar na shekarar bana

- Makinde yace ba abin da Gwamnatin ta shiryawa matasa da sauran Jama’a

Wani ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Oyo a karkashin Jam’iyyar PDP Injiniya Seyi Makinde yayi kaca-kaca da kasafin kudin da Gwamnan Jihar Abiola Ajimobi ya gabatar a gaban Majalisa.

Dan takarar PDP ya soki kasafin kudin Jihar Oyo na 2018

Kwanan nan aka daure tsakanin Iyalin Ganduje da na Ajimobi

Dan takarar PDP Seyin Makinde ya soki kasafin kudin Jihar Oyo na 2018 wanda yace zai kara jefa matasa da sauran jama'an Jihar ne cikin wani halin ha’ula’i. Makinde yayi wannan jawabi ne ta bakin wani daga cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben sa.

KU KARANTA: Shugaban Najeriya Buhari ya daga kofin Duniya

Gwamna Abiola Ajimobi ya ware abin da bai wuce kashi 3% ba kan harkar noma in da ya warewa ofishin sa akalla Naira Biliyan 15 daga kasafin na bana. Kudin dai da aka warewa ofishin Gwamna ya zarce abin da aka warewa sha’anin lafiya da kuma ilmin zamani.

‘Dan siyasar dai yana gani bai dace a warewa harkar noma da kiwo Naira Biliyan 270 ba kacal ganin yadda ake da manoma da dama a Jihar ga kuma rikicin makiyaya da ake ta fama da shi. Yace jama’a su shirya don wahala ba ta kare masu ba a Gwamnatin APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel