Nigerian news All categories All tags
Rikicin jihar Benuwe: Jami’an tsaro sun cafke makiyaya guda 44 masu kiwo a cikin gari

Rikicin jihar Benuwe: Jami’an tsaro sun cafke makiyaya guda 44 masu kiwo a cikin gari

Hukumar Yansandan jihar Filato ta sanar da cafke makiyaya guda 44 a yankuna daban daban na jihar Benuwe da suka yi ma dokar hana kiwo da gwamnatin jihar ta tabbatar, inji rahoton Daily Trust.

Kwamishinan Yansandan jihar, Fatai Owoseni ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labaru yace jami’an rundunar Soji ne suka kama maiyayan, daga bisani suka mika su ga jami’an Yansanda, inda yace a yanzu haka sun gurfanar dasu gaban kuliya manta sabo don amsa laifukansu.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane, barayin shanu da yan fashi da makami 50 sun fada komar Yansanda a Katsina

A wani labarin kuma, Kwamishinan yace Yansandan Najeriya sun kama wasu mutane guda 10 bayan sun samu rahotanni daga wasu makiyaya mazauna karamar hukumar Guma na jihar,inda suka yi zargin an sace musu dabbobi.

Rikicin jihar Benuwe: Jami’an tsaro sun cafke makiyaya guda 44 masu kiwo a cikin gari

Yansanda

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kwamishinan yana fadin cewa bayan sun kama wadanda ake zargi da satar shanun, sun kuma yi kokarin kwantar da duk wata tarzoma da ka iya tasowa saboda haka, haka zalika rundunar na cigaba da inganta alaka tsakaninta da sauran hukumomin tsaro.

Daga karshe kwamishinan ya bayyana cewa rundunar Yansandan jihar za tayi iya bakin kokarinta don ganin ta jaddada dokar hana kiwo a cikin garin Benuwe don tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Idan za’a tuna, rikicin makiyaya da manoma da ya addabi jihar Benuwe ya janyo mutuwa jama’a da dama tare da asarar dukiyoyi a jihar tun a shekarar data gabata, sai dai shugaban kasa Buhari ya bada tabbacin kawo karshen hare haren.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel