Shari’a saɓanin hankali: Alkalin Kotu ya yanke ma wani ƙaramin Yaro hukuncin shara

Shari’a saɓanin hankali: Alkalin Kotu ya yanke ma wani ƙaramin Yaro hukuncin shara

Wata Kotun majistri dake zamanta a unguwar Gyadi gyadi na jihar Kano ta yanke ma wani dalibin dan aji shida da ba’a bayyana sunansa ba, hukuncin sharan farfajiyar Kotun, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an gurfanar da wannan yarone gaban Kotun kan wasu tuhume tuhume guda biyu da ake tuhumarsa da su, da suka hada da fasa shago da kuma sata, wadanda suka ci karo da sassa 342 da 286 na kundin hukunta laifuka na jihar Kano.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane, barayin shanu da yan fashi da makami 50 sun fada komar Yansanda a Katsina

Dansanda mai kara ya shaida ma Kotun cewa a ranar18 ga watan Feburairu ne wani mutum mai suna Muhammad Sani mazaunin unguwa uku, ya kai kara zuwa ofishin Yansandan cewa yaron ya fasa masa shago inda aka tafka masa sata.

Muhammad Sani ya bayyana ma Kotun cewa Yaron ya sace masa galolin mai guda biyar, sai dai babu komai a cikinsu, amma darajarsu ta kai N3,500 a duk guda, hakazalika dumu dumu aka kama shi da su.

Sa’nnan da aka karanto masa laifukan da ake tuhumarsa da su, sai yaron ya kada baki ya amsa laifukan gaba daya, daga nan sai Alkali Hajara Garba ta yanke masa hukuncin shara, inda ta umarce shi ya share farfajiyar Kotun na tsawon awanni guda 3, daga nan sai ta sallame shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: