Nigerian news All categories All tags
Fastocin takarar Shugaban kasa na Dino Melaye sun fara yawo a gari

Fastocin takarar Shugaban kasa na Dino Melaye sun fara yawo a gari

- Fostocin takarar Sanatan Kogi Dino Melaye sun fara yawo a kasa

- Sai dai fitaccen 'Dan Majalisar yace wannan sam ba aikin sa bane

- Sanatan dai ya taba furta cewa zai nemi takarar kujerar wata rana

Mun samu labari cewa a makon nan ne aka fara ganin fastocin yakin neman zaben Sanatan Jihar Kogi ta yamma watau Dino Melaye wanda babban na hannun-daman Bukola Saraki ne a Majalisa Dattawa.

Fastocin takarar Shugaban kasa na Dino Melaye sun fara yawo a gari

Sanata Dino Melaye yace bai da shirin takarar Shugaban kasa

A makon can ne fostocin 'Dan Majalisar su ka cika gari inda aka ga Sanatan ya sa kaftani da kuma hula inda yake neman a zabe sa a matsayin Shugaban kasa a 2019 da sunan cewa ya kamata a kauda tsofaffin Shugabanni.

KU KARANTA: Ana iya yin juyin mulki a wannan zamani inji Ekweremadu

A fostocin an yi kira ga Jama'a su zabi yara masu katabus da tunanin cigaban kasa. Wadannan fastocin dai sun ba Jama'a mamaki ko da yake an san tsohon 'Dan Majalisar Wakilan kasar da shiga cikin abin magana a Kasar.

Tuni dai Dino Melaye ya zare hannun sa daga wannan fastocin yace ba aikin sa bane. Ko da dai Sanatan ya taba cewa zai nemi takarar Shugaban kasa wata rana, yace wannan karo ba aikin kowa bane sai Makiyan sa a siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel