Kwakwkwafi: Sanatan Najeriya ya bankado adadin tiriliyoyin da jam'iyyun APC da PDP kowacce ta ranto

Kwakwkwafi: Sanatan Najeriya ya bankado adadin tiriliyoyin da jam'iyyun APC da PDP kowacce ta ranto

- Sanatocin Najeriya sun fusata saboda shugaba Buhari ya ki amincewa da kudirin kirkirar Peace Corps

- Sun ce ba gaskiya ba ne gwamnatin Najeriya ta ce matsalar kudi ta hana ta zartar da kudirin

- Sanata Dino Melaye ya ce APC ta ranto tiriliyan 11 cikin shekaru uku kacal

Sanatocin Najeriya sun fusata a kan kin amincewar da shugaba Buhari ya yi a kan kudirin kirkirar Peace Corps.

Sanatocin sun bayyana cewar ba gaskiya ba ne gwamnati ta fake da batun rashin kudi, su na masu bayyana cewar ko a lokacin da aka so kirkirar Civil defense haka gwamnatin wancan lokaci ta fada.

Kwakwkwafi: Sanatan Najeriya ya bankado adadin tiriliyoyin da jam'iyyun APC da PDP kowacce ta ranto

Dino Melaye

Da yake martani a kan batun, Sanata Dino Melaye ya ce kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali wajen kirkirar guraben aiyuka ga matasa.

Sanata Melaye ya bayyana cewar gwamnatin APC, cikin shekaru uku kacal, ta ranto tiriliyan N11tn amma ta na korafin rashin isassun kudin da zata rike hukumar Peace Corps idan an kirkire ta.

DUBA WANNAN: Akwai Yunwa Haram a wannan gwamnatin - Sule Lamido

Ya kara da cewar jam'iyyar PDP ta ranto tiriliyan N6tn ne cikin shekaru 16 amma duk da haka ta iya kirkirar hukumar civil defence.

Melaye ya ce hatta biliyan N500bn da gwamnatin ta ware karkashin shirin nan na N-POWER ba ta canja komai ba a kasar nan.

Majalisar ta ce zata aike da wani sako na musamman ga shugaba Buhari domin ba shi shawarar ya sake nazarin kudirin kirkirar Peace Corps.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel