Nigerian news All categories All tags
2019: Babu abin da zai hana surikina hawa kujerar mulki - Rochas Okorocha

2019: Babu abin da zai hana surikina hawa kujerar mulki - Rochas Okorocha

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana cewa babu wani abu da zai zamo Katanga wajen kare surikinsa Uche Nwosu daga zama gwamna.

Ya jaddada cewa lallai shine zai gaje shi a zaben 2019.

A wata sanarwa daga kakakin gwamnan, Mista Sam Onwuemeodo ya bayyana cewa duk wani cece-kucen da ake yayatawa ba zai hana shi tsayar da surikin nasa ba a zaben 2019.

2019: Babu abin da zai hana surikina hawa kujerar mulki - Rochas Okorocha

2019: Babu abin da zai hana surikina hawa kujerar mulki - Rochas Okorocha

Ya ce Allah ya rigada ya nufa sannan kuma mutanen jihar baki daya na kaunarsa.

KU KARANTA KUMA: Ziyarar da Buhari ya shirya kaiwa Benue da sauransu duk kamfen ne - PDP

A halin da ake ciki Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin kaiwa jihohin Benue, Taraba da sauran inda aka kashe yan Najeriya da dama a matsayin kamfen din zaben 2019.

A wata sanarwa daga PDP ta hannun kakakinta, Kola Ologbondiyan tace abun mamaki ne yadda Buhari ya yanke shawarar ziyartan wadannan jihohi bayan kungiyoyin makasa, yan ta’adda da kuma yan fashi sun aikata ta’asarsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel