Harin bom – Kotu ta yanke wa Charles Okah hukuncin daurin rai da rai

Harin bom – Kotu ta yanke wa Charles Okah hukuncin daurin rai da rai

- Kotu ta yankewa dan uwan tsohon shugaban kungiyar masu neman 'yanci Neja Delta hukuncin daurin rai da rai

- Henry Okah yana cikin mutanen da suka dauki nauyin kai harin bom din da aka yi a ranar bikin yanci kai na Najeriya a lokacin mulkin Jonathan

Babban kotun tarayya dake zama a Abuja ta yanke wa, Charles Okah, da mataimakin sa, Obi Nwabueze, daurin rai da rai a gidan kaso bisa laifin daukar nauyin harin bom din da ya tashi a ranar bikin samun ‘yancin Najeriya, na shekara 2010 a birnin Abuja, da kuma wanda da ya tashi a Warri a jihar Delta a watan Mayu na shekara 2010.

Legit.ng ta samu rahoton cewa masu laifin sun shirya harin ne tare da dan uwan Charles Oka, mai suna, Mista Henry Okah, wanda shine tsohon shugaban kungiyar masu neman ‘yancin yankin Neja Delta MEND.

Harin bom – Kotu ta yanke wa Charles Okah hukuncin daurin rai da rai

Harin bom – Kotu ta yanke wa Charles Okah hukuncin daurin rai da rai

Shi kuma Henry, Okah kotun kasar Afrika ta kudu ta yanke masa hukuncin shekaru 24 a gidan kaso.

KU KARANTA : Afenifere da kungiyar CDHRH sun mayar da martani akan maganar da Buhari yayi akan rikicin Taraba

Akalla mutane 12 suka rasa rayukan a harin bom da su Okah suka kai wa birnin Abuja a shekara 2010.

Harin ya auku ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel