Nigerian news All categories All tags
2019: Sultan ya bukaci Musulmai da su mallaki katin zabe

2019: Sultan ya bukaci Musulmai da su mallaki katin zabe

Sultan na Sokoto kuma sarkin Musulmi na kasa, Alhaji Abubakar Saad 111, ya bayyana bukatar dukkan Musulmai da suyi amfani da damar rijistan zabe da akeyi domin su mallaki katin kafin zaben 2019.

Da yake Magana a taron gasar Al-Qur’ani na kasa karo na 32 a Katsina, Sultan ya ce ta hanyar mallakar katin ne kadai mutane zasu iya samun shugabannin da suke ra’ayi.

“Mu samu mu mallaki katunan zabenmu saboda da shine zamu iya samun abunda muke buri. Mutane zasu zo neman kuri’unmu sannan ne zamu fada masu abunda muke bukata daga gare su”, inji shi.

2019: Sultan ya bukaci Musulmai da su mallaki katin zabe

2019: Sultan ya bukaci Musulmai da su mallaki katin zabe

KU KARANTA KUMA: Ziyarar da Buhari ya shirya kaiwa Benue da sauransu duk kamfen ne - PDP

Ya kalubalanci shugabanni da su ji tsoron Allah da mabiyansu kuma. A nasa jawabin, gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya ce ya zama dole masu ruwa da tsaki suyi duba ga karatun almajiranci.

A halin yanzu, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin kaiwa jihohin Benue, Taraba da sauran inda aka kashe yan Najeriya da dama a matsayin kamfen din zaben 2019.

A wata sanarwa daga PDP ta hannun kakakinta, Kola Ologbondiyan tace abun mamaki ne yadda Buhari ya yanke shawarar ziyartan wadannan jihohi bayan kungiyoyin makasa, yan ta’adda da kuma yan fashi sun aikata ta’asarsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel