Jami’an hukumar NDLEA sun bankado maka-makan gonakan tabar wiwi guda 5 a Jigawa

Jami’an hukumar NDLEA sun bankado maka-makan gonakan tabar wiwi guda 5 a Jigawa

Hukumar yaki sha da tu’ammali da miyagun kwayoyi, NDLEA ta gano wasu maka makan gonakai guda biyar inda ake nomo tabar wiwi, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin hukumar, Asuquo Nkereuwem ya bayyana haka a ranar Laraba7 ga watan Feburairu, inda yace an gano gonakan ne biyo bayan leken asiri da jami’an hukumar ta yi.

KU KARANTA:Hanyoyi 5 da za’a iya bi don kubuta daga kamuwa daga cutar zazzabin Lassa

“A kokarin mu kawar da miyagun kwayoyi da Najeriya tare da fatattakar dillalan wiwi a jihar Jigawa, mun gano wasu gonaka daban daban guda biyar da ake noma tabar wiwi a kauyukan Kagadam, Tsagan da wasu kauyuka guda 3 a karamar hukumar Ringim.” Inji shi.

Kaakaki yace manoman wiwi sun hada shi ne tare da albasa, tumatir da sauran kayan lambu don kada a gane, inda ya kara da cewa sun samu nasarar cafke guda cikin manoman a ranar 26 ga watan Feburairu a kauyen Kagadam dauke da kilo 12.5 na tabar wiwi da ya ciro daga gonar.

Bugu da kari Kaakakin yace sun lalata daya daga cikin gonakab, yayin da masu sauran gonakai guda uku suka lalata abinsu da kansu don gudun shiga hannun jami’an hukumar NDLEA. Daga nan kuma yayi kira ga gwamnati data samar musu da motoci da Babura don gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Daga karshe yace zasu gudanar da bincike kan lamarin, da zarar an kammala za’a gurfanar da wanda ala kama gaban Kotu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel