Nigerian news All categories All tags
Hukumar lekan asiri ta NIA suna farautar wani Jakadan Najeriya

Hukumar lekan asiri ta NIA suna farautar wani Jakadan Najeriya

- Hukumar NIA ta na farautar tsohon Darakta Janar na hukumar Mohammed Dauda

- Mohammed Dauda ya rike mukamin Darakta Janar na hukumar NIA na tsawon watannin shida

Jami’an hukumar lekan asiri na NIA sun shiga farautar Jakadan Najeriya a kasar Chadi sakamakon shaidar karya da y aba kwamiti bincike na majalissar Tarayya a shekarar 2017.

A shekarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta kira jakada, Mohammed Dauda daga, kasar Kamaru, ta na da shi Daraektan hukumar NIA na rikon kwarya, bayan an dakatar da tsohon Daraektan hukumar, Mista Ayo Oke, sakamakon makudan kudaden da aka samu a cikin gidan matar sa dake unguwar Ikoyi a jihar Legas.

Dauda ya riki mukamin Daraekta JaNar na hukumar NIA na tsawon watanni shida kafin aka maye gurbin sa da, Ahmed Rufai Abubakar.

Hukumar lekan asiri ta NIA suna farautar wani Jakadan Najeriya

Hukumar lekan asiri ta NIA suna farautar wani Jakadan Najeriya

Daganan sai gwamnatin tarayya ta umarci, Mohamed Dauda, da ya koma matsayin sa na farko a kasar Chadi ya ci gaba da aikin da ya ke yi a can.

KU KARANTA : Afenifere da kungiyar CDHRH sun mayar da martani akan maganar da Buhari yayi akan rikicin Taraba

Dauda bai koma ba, ya bada dalilin cewa rayuwar sa a Chadi za ta shiga cikin hadari, yanzu kowa ya san cewa shi tsohon jami’in Hukumar NIA ne.

Hukumar NIA ta ce ta na farautar sa ne bayan ya ki halarta gayyatar da kwamitin binciken ta yi masa bisa zargin tona asiri, da zubar da mutuncin hukumar NIA a idon jama’a.

NIA ta zargi da Dauda da fada wa hukumar EFCC cewa, Babagana Kingibe ya na diba makudan kudade daga asusun hukumar NIA yana dankara wa farkar sa dake kasar waje, amma Kingibe ya karyata wannan zargi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel