Nigerian news All categories All tags
Ziyarar da Buhari ya shirya kaiwa Benue da sauransu duk kamfen ne - PDP

Ziyarar da Buhari ya shirya kaiwa Benue da sauransu duk kamfen ne - PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin kaiwa jihohin Benue, Taraba da sauran inda aka kashe yan Najeriya da dama a matsayin kamfen din zaben 2019.

A wata sanarwa daga PDP ta hannun kakakinta, Kola Ologbondiyan tace abun mamaki ne yadda Buhari ya yanke shawarar ziyartan wadannan jihohi bayan kungiyoyin makasa, yan ta’adda da kuma yan fashi sun aikata ta’asarsu.

Ziyarar da Buhari ya shirya kaiwa Benue da sauransu duk kamfen ne - PDP

Ziyarar da Buhari ya shirya kaiwa Benue da sauransu duk kamfen ne - PDP

“Shugaban kasa ya kasance a kasar nan sannan kuma bai taba tunanin ya kamata ya ziyarci jihohin da ta’asar ya afka mawa ba har sai da yan Najeriya suka shirya juya masa baya.

“Abun ma da ya fi taba zuciya shine a jihar Benue, shugaba Buhari ya aika sammaci ga shugabannin al’umma zuwa fadar shugaban kasa, Abuja maimakon ya yi koyi ga tsohon al’addan yan Afrika ta hanyar ziyartan su.

KU KARANTA KUMA: Inda yar fim din Hausa ce tayi wannan tsiyar ta yar Ganduje da Kaji ana zagi da tofin Allah tsine – Fati Muhammed

“Lallai shiyasa yan Najeriya suka nuna shirin ziyarar shugaba Buhari zuwa wadannan jihohi a matsayin ihu bayan hari. Yan Najeriya sun rigada sun nuna ra’ayinsu akan sa, kuma hakan ne, a matsayinsa na shugaban kasa bai taba nuna damuwarsa akan su ba a lokacin da suke bukatar hakan” cewar jam’iyyar adawan.

A halin yanzu mun samu labari cewa Shugaban Kungiyar NAC ta Najeriya Dr. Oladope Agoro ya ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara da ya hakura da neman zarcewa a kan mulki kurum koma gida.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel