Kotun Najeriya ta fitar da sabbin ka'idojin a kan tallar kwaroron roba

Kotun Najeriya ta fitar da sabbin ka'idojin a kan tallar kwaroron roba

- Kotun Najeriya ta umarci dukkan a rubuta cewar kauracewa jima'i ne ya fi alheri a duk tallar kwaroron roba

- Kazalika kotun ta ce daga yanzu za a ke tallata kwaroron roba ne daga karfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na yamma a gidajen radiyo da kuma karfe 6:0 na yamma 10:00 na dare a gidajen talabijin

- Alkalin wata kotu a Legas, Taofiquat Oyekan-Abdullahi ne ya zartar da wannan hukunci bayan karar da wata kungiya ta shigar da hukumar kiyaye lafiyar iyali (SFH)

Wata babbar kotu a Legas ta zartar da hukuncin cewar dole daga yanzu a rubuta a duk tallar kwaroron roba cewar kauracewa jima'i ne ma fi alheri a kan amfani da kororon roba.

Kotun ta ce kwaroron roba ba ya bayar da kariya dari bisa dari.

Alkalin kotun, Taofiquat Oyekan-Abdullahi, ne ya zartar da wannan hukunci bayan karar da wata kungiya mai rajin kare lafiyar al'umma (PHD) ta shigar a gabanta ta hannun lauyanta, Sonnie Ekwowusi.

Kotun Najeriya ta fitar da sabbin ka'idojin a kan tallar kwaroron roba

Kwaroron roba

Kotun ta ce daga yanzu za a ke tallata kwaroron roba ne daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 8:00 na dare a gidajen radiyo da kuma karfe 6:00 na yamma zuwa 10:00 na dare a gidajen talabijin.

DUBA WANNAN: An samu ma'aikacin banki da hannu dumu-dumu cikin badakalar fiye da miliyan N700m

Kotun ta bayyana cewar kin yin biyayya ga wannan hukunci laifi da ya saba da doka da kuma kundin tsarin mulkin kasa.

Kungiyar PHD ta ce, bayan wannan hukunci na kotu, duk wanda ya dogara da kororon roba domin kariya, to ya ku ka da kansa duk abinda ya biyo baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel