Nigerian news All categories All tags
Tonon silili: Shehu Sani ya fallasa abinda gwamnati ke biyan Sanatocin Najeriya a duk wata

Tonon silili: Shehu Sani ya fallasa abinda gwamnati ke biyan Sanatocin Najeriya a duk wata

Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya arin sanatocin Najeriya yaci musu albasa, inda ya bayyana cewar ana biyan kowanne sanata naira miliyan 13.5 a matsayin kudin tafiyar da al’amura, bayan albashinsu.

Shehu Sani ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da wata kafar sadarwar ta The News, inda yace wannan kudin tafiyar da al’amura da ake basu ya tasan ma naira miliyan goma sha uku da dubu dari biyar, bayan albashinsu da ya kai dubu dari bakwai (700,000).

KU KARANTA: An hallaka mutane 24 sakamakon wata sabuwar rikici da ta ɓarke a jihar Benuwe

“Zan iya cewa kudin tafiyar da al’amura da ake baiwa kowanne sanata ya kai naira miliyan 13.5 a kowanne wata.” Kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Sanatan ya cigaba da fadin duk da yake ba’a kayyade yadda ya kamata Sanata ya kashe wadannan kudade ba, amma ana bukatar kowanne Sanata ya kawo shaidar kashe kudaden, wato rasit, kuma yace ana basu kudin yi ma al’ummarsu ayyuka na musamman.

Tonon silili: Shehu Sani ya fallasa abinda gwamnati ke biyan Sanatocin Najeriya a duk wata

Shehu Sani

“Kudin da zaka iya kashewa ba tare da wan tuhuma ba shine albashinka, 700,000, bugu da kari za;a kashe ma Sanata kudi naira miliyan 200 don ayyukan mazabarsa, sai dai ba kudin ake bashi a hannu ba, fada mana ake akwai kudi miliyan N200,000 a hannun wata ma’aikata, mu kuma sai mu kai musu ayyukan da muke bukata a yankin namu, sai ma’aikatar ta yi su.” Inji shi.

Sai dai Sanatan yace shi kam “Ina kira da a daina biyan wannan naira miliyan 13.5, a bar mu kawai da albashinmu, amma fa su ma jama’a a fada musu su daina binmu gida gida suna neman kudi. Haka zalika ban gamsu a ce wai da yan majalisa ake gudanar da ayyukan mazabu ba, ba yin dokoki bane kadai aikinmu?

“Abin haushin shi ne, a siyasar Najeriya, duk dan majalisan da bai yi ma jama’ansa aiki ba, toh ba zasu gode masa ba, wanda abin ba haka yake a Amurka ba, hakan na faruwa ne saboda bakin talauci da al’ummar mu suke ciki, don haka su kawai ka basu kudi, kuma ka kawo musu ayyuka.” Inji shi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel