Gwamnati ta ware N800m don koyar da larabci da addinin musulunci - Minista

Gwamnati ta ware N800m don koyar da larabci da addinin musulunci - Minista

- Gwamnatin Tarayyah ta ware makudden kudi don inganata ilimin larabci da addinin musulunci

- Ministan Ilimi na kasa, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a taron kadamar da hedkwatan hukumar a garin Kaduna

- Hukumar ne ka da alhakin kulawa da tsara jarabawa na harshen larabci da kuma darussan addinin musulunci a duk fadin Najeriya

Gwamnatin tarayyah ta bayyana cewa ta ware sama da kudi N600m a kasafin kudin shekarar 2018 don gudanar da manyan ayyuka a Hukumar Kula da Koyar da Larabci da addinin musulunci (NBAIS).

Hakazalilka, Gwamnatin ta kuma ware N200m don gyaran gine-ginen hukumar da ta gada daga gwamnatin da ta shude kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta ware N800m don koyar da larabci da addinin musulunci - Minista

Gwamnatin ta ware N800m don koyar da larabci da addinin musulunci - Minista

KU KARANTA: Wani direba ya halaka jami'in 'dan sanda a Legas

A jawabin da yayi yayin kaddamar da hedkwatan hukumar a garin Kaduna, Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya ce gwamnati na kokarin shigar da sunayen ma'aikatan hukumar cikin tsarin biyan albashi na IPPIS wanda zai lashe kudi kimanin N2bn duk shekara.

Hukumar NBAIS ne ka da alhakin kulawa da tsara jarabawa na harshen larabci da kuma darussan addinin musulunci a duk fadin kasar nan. An kafa hukumar ne a shekarar 1960 a karkashin Hukumar Ilimi na Arewacin Najeriya sannan daga baya da zama sashi na musamman karkashin Hukumar Ilimi na Tarayya a 2017.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel