Nigerian news All categories All tags
An samu ma'aikacin banki da hannu dumu-dumu cikin badakalar fiye da miliyan N700m

An samu ma'aikacin banki da hannu dumu-dumu cikin badakalar fiye da miliyan N700m

- Wata kotu dake Ikeja a jihar Legas ta samu wani ma'aikacin bankin Coronation Merchant Bank da badakalar wawure kudi

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da ma'aikacin bankin da badakalar kudin da adadin su ya kai miliyan N700m

- Ma'aikacin bankin ya wawure kudin ta hanyar yaudara da satar sa hannun masu ajiya a bankin

Wata kotu dake Ikeja a jihar Legas ta samu wani ma'aikacin bankin Coronation Merchant Bank, Nsa Ayi, da laifin wawure kudin masu ajiya da yawansu ya kai miliyan N700m.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta a gurfanar da ma'aikacin bankin a ranar 26 ga watan Fabrairu bayan ta same shi da laifin hada baki da wasu mutane tare da yin sama da fadi da adadin kudaden.

An samu ma'aikacin banki da hannu dumu-dumu cikin badakalar fiye da miliyan N700m

An samu ma'aikacin banki da hannu dumu-dumu cikin badakalar fiye da miliyan N700m

Alkalin kotun, mai shari'a Mojisola Dada, ya tabbatar da samun Ayi da aikata dukkan caji 11 da ake yi masa kamar yadda ya amsa da bakinsa.

EFCC ta shaidawa kotun cewar Ayi ya wawure wasu kudin ta hanyar satar sa hannun masu ajiya a bankin tare da karkatar da kudin ajiyar su zuwa wasu asusu dake bankin Guaranty Trust da Zenith Bank.

DUBA WANNAN: Za a fara amfani da yaren uwa wajen koyar da yara a makarantun firamare

A farko bayan gurfanar da shi, Ayi, ya ce bai aikata laifin da ake zargin sa da aikatawa ba kafin daga bisani ya amsa laifinsa yayin zaman kotun na jiya, Talata.

Lauyan dake kare Ayi, Robert Clarke, ya ce wanda yake karewa ya canja matsayinsa na baya ne bayan wata ganawa ta sirrri da su ka yi.

Alkali Mojisola Dada ya tsayar da ranar 22 ga watan Maris domin yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel