Nigerian news All categories All tags
Kwamandan Boko Haram da hukuma ta saki domin sako yan matan Chibok ya yi barazana ga gwamnatin Najeriya

Kwamandan Boko Haram da hukuma ta saki domin sako yan matan Chibok ya yi barazana ga gwamnatin Najeriya

Shuaibu Moni, wannan kwamandan na kungiyar Boko Haram wanda hukuma ta saki a musanyan yan matan Chibok wanda gwamnatin kasar Sweden ta sa baki a watan Mayun da ya gabata ya fara barazana ga gwamnatin Najeriya.

A wani sabuwar faifan bidiyo da Sahara Reporters ta samu na nuna Shuaibu Moni da wasu yaransa a dajin Sambisa inda yake jawabi a yaren Hausa da Larabci, Moni ya ce sabanin rahotannin da ke yaduwa cewa an fittiki yan Boko Haram daga dajin Sambisa karya ne.

Ya bayyana cewa mambobin kungiyar na nan daram dam-dam a cikin dajin Sambisa.

Kwamandan Boko Haram da hukuma ta saki domin sako yan matan Chibok ya yi barazana ga gwamnatin Najeriya

Kwamandan Boko Haram da hukuma ta saki domin sako yan matan Chibok ya yi barazana ga gwamnatin Najeriya

A jawabin, ya yi barazana ga gwamnatin Najeriya cewa cikin kwanaki masu zuwa, za su kai munanan hari a Najeriya.

KU KARANTA: Allah ya kiyaye, Saura kiris sabuwar rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarabawa a Ile-Ife

Moni ya bayyana cewa bangaren kungiyar da yan matan Abu Musab al-Barnawi ke jagoranta ne suka sace yan matan Dapchi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel