Nigerian news All categories All tags
Hukumar Sojin Sama ta tanadi sabbin mahallai ga dakarun ta a jihar Neja

Hukumar Sojin Sama ta tanadi sabbin mahallai ga dakarun ta a jihar Neja

A sakamakon fafutikar ta na inganta jin dadin dakaru, hukumar Sojin Sama a ranar Larabar da ta gabata ta tanadar tare da kaddamar da wasu sabbin mahallai a birnin Minna na jihar Neja.

Kakakin hukumar, Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya, shine ya bayyana hakan a shafin sada zumuntar facebook na hukumar, inda ya bayyana cewa hukumar ta yi wannan hobbasa ne domin dadadawa ma'uratan dakaru da kuma daya-dayansu marasa aure.

Sabbin mahallai da hukumar ta tanadar

Sabbin mahallai da hukumar ta tanadar

Sabbin mahallai da hukumar ta tanadar

Sabbin mahallai da hukumar ta tanadar

Air Vice Marshal Ibrahim Yahaya, shine ya kaddamar da wannan sabbin mahallai a yayin da ya wakilci shugaban hafsin sojin Sama, Air Marshal Sadique Abubakar.

Shugaban hafsin sojin saman ya bayyana cewa, wannan yunkuri yana daya daga cikin muhimman manufofi da shugabacin hukumar ya sanya a gaba.

KARANTA KUMA: Rikicin Matasa ya salwantar da rayuka 3 a jihar Filato

Ya kuma nemi dakarun da rabon su ya tsaga da su yi tattalin wannan mahallai tare da jajircewa wajen sauke nauyin bai wa kasar nan kariya da ya rataya a wuyan su.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar sojin kasa ta kaddamar da wani sabon bariki mai sunan 16 Brigade Camp Buratai a jihar Bayelsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel