Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau

Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa tarayya a yau Laraba, 7 ga watan Maris 2018 a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa, babban birnin tarayya Abuja.

Shugaba Buhari yana jagoranta wannan zama ne bayan ya kai ziyara kasar Ghana domin halartan taron murnan zagayowar ranan samun yanci kai na kasar Ghana.

Shugaban kasan Najeriya yayiwa kasar Ghana alkawarin cewa zai taimaka musu wajen yakin cin hancin da rashawa, amma da alamun wannan magana bai yiwa mutan kasar Ghana dadi ba.

Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau

Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau

Daga cikin wadanda suka halarci taron majalisar sune ministan ma'adinai, Kayode Fayemi; ministan sufuri, Rotimi Amaechi; ministan ayyuka ruwa, Abubakar Bwari; ministan Ayyuka, wutan lantarki da gidaje, Babatunde Raji Fashola.

Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau

Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa a yau

Sauran sune ministan kwagado, Chris Ngige; babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Babagana Munguno; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan gwamnati, Oyo Ita.

KU KARANTA: Rikicin Taraba ya fi na Benuwe da Zamfara muni – Buhari

Majalisar zantarwa tarayya ta kunshi dukkan ministocin gwamnati, manyan masu baiwa shugaban kasa shawara, masu magana da yawunsa, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, shugaban ma’aikatan gwamnati, sakataren gwamnatin tarayya da kuma duk wani mai fada aji a fadar shugaban kasa.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel