Nigerian news All categories All tags
Sanata Ben Bruce yayi wa Buhari ba’a akan yiwa kasar Ghana alkawarin taya su yaki da cin hanci da rashawa

Sanata Ben Bruce yayi wa Buhari ba’a akan yiwa kasar Ghana alkawarin taya su yaki da cin hanci da rashawa

- Shugaba buhari ya halarci bikin cika shekaru 61 da kasar Ghana ta samu 'yancin kai

- Buhari yayi alkawarin taya kasar Ghana yaki da Cin hanci da rashawa

Ben Bruce, Sanata mai wakiltar mazabar kudancin Bayelsa, ya mayar da martani akan jawabin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi a kasar Ghana.

Da yake jawabi a lokacin da ya halarcin bikin cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai da kasar Ghana ta yi a ranar Talata, shugaba Buhari yayi alkawarin taimakawa kasashen Afrika ta yamma yaki da cin hanci da rashawa.

Sanata Ben Bruce, ya mayar da martani da cewa, shugaban kasa ya fara yakar cin hanci da rashawa a kasar tukun kafin yaje wata kasa.

Sanata Ben Bruce yayi wa Buhari ba’a akan alkawarin taya kasar Ghana yaki da cin hanci da rashawa da yayi

Sanata Ben Bruce yayi wa Buhari ba’a akan alkawarin taya kasar Ghana yaki da cin hanci da rashawa da yayi

Bruce yace Buhari ya sa Najeriya ta zama abun dariya ga kasashen duniya. Cin mutuncin ‘yan adawa shine yake kira yaki da cin hanci da rashawa.

KU KARANTA : Noman shinkafa : Audu Ogbe yayi karya – Jakadan kasar Thailand

Ben Bruce ya bayyana haka ne a shafin sa na Tuwita a ranar Laraba .

A ranar Litinin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ziyarci kasar Ghana dan halarta bikin cika shekaru 61 da kasar Ghana ta yi a ranar Talata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel