Nigerian news All categories All tags
Gumi ya bayyana hanya daya tilo da sojoji za su bi don cin galaba kan Boko Haram

Gumi ya bayyana hanya daya tilo da sojoji za su bi don cin galaba kan Boko Haram

- Shahararen malamin addinin musulunci, Sheikh Abubakar Gumi ya shawarci Hukumar Sojin Najeriya ta kirkiri rundunar musulmi na musamman da za ta yaki Boko Haram

- Ya ce rundunar da za'a kirkira za tayi amfani da ka'idoji da dabaru irin na addinin Islama wajen yaki da Boko Haram

- Babban Malamin ya ce ba za'a iya cin galaba kan Boko Haram har sai an bi ka'idojin yaki irin na addinin musulunci

Shahararen malamin addinin musulunci mazaunin garin Kaduna, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, ya yi kira da a ba wa Malamai dama a bangaren Sojojin Najeriya don taimakawa wurin yakar yan Boko Haram bisa ka’idojin addinin Musulunci.

Sheikh Gumi ya kara da cewa, kowane bangaren na yakin zai zama karkashin jagorancin Malamin Addini, ya ce baza’a taba cin nasara a yaki da ‘yan kungiyar ba idan har ba ka’idojin addinin musulunci akayi amfani dasu ba.

Sheikh Gumi ya shawarci sojojin Najeriya kan yadda za'a ci galaba kan Boko Haram

Sheikh Gumi ya shawarci sojojin Najeriya kan yadda za'a ci galaba kan Boko Haram

KU KARANTA: Kotu ta daure shi na watanni 5 don ya ma makwabcin sa sata

Malamin ya ce, wasu daga cikin matakan Jami’an na mu suna shiga cikin rudani, shiyasa duk sanda ‘Yan kungiyar ta Boko Haram su ka fadi Allahu Akbar (Allah mai girma), wasu daga cikin Sojojin namu sai kaga sun watsar da makaman na su sun zuba a guje. Amma idan muna da musulmai a karkashin jagorancin Malamai, za su yi yaki ne a matsayin Jihadi.

Ina ganin idan muka jaraba wannan shawarar zai kawo karshen tashin hankula. Abun yana bani mamaki, saboda haka dole muyi amfani da ka’idoji na Addini wurin wannan yakin. Shaikh Gumi ya kuma ce, musulmai ne kadai zasu iya yakar Boko Haram a Arewa maso Gabacin Najeriya, har ma a duniya baki daya.

Mashahurin Sheikh din yace akwai bukatar kungiya tsakanin Musulmai da sauran Addinai don kawo karshen wannan ta’addanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel