Nigerian news All categories All tags
EFCC ta karbi $375,000 da jami'an kwastam suka kwace a garin Kaduna

EFCC ta karbi $375,000 da jami'an kwastam suka kwace a garin Kaduna

Jami'an rundunar hana fasa-kwauri ta kasa watau kwastam ta mikawa hukumar nan dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC zunzurutun kudi har dalar Amurka dubu 375 da suka kwace daga hannun wani mai suna Adamu Rabiu Muhammad a jiya Talata, 6 ga watan Maris, 2018.

Shi dai Adamu Rabiu dake zaman wani hamshakin dan kasuwa a garin Kano kamar yadda muka samu rundunar jami'an kwastam din ce ta shiyyar Kaduna suka damke shi a filin jirgin sama na kasa-da-kasa dake a garin na Kaduna.

EFCC ta karbi $375,000 da jami'an kwastam suka kwace a garin Kaduna

EFCC ta karbi $375,000 da jami'an kwastam suka kwace a garin Kaduna

KU KARANTA: Dan Zamfara ya zama sanata a Italiya

Legit.ng ta samu cewa shugaban hukumar ta EFCC da yake jawabin sa ya godewa rundunar jami'an kwastam din bisa namijin kokarin da suke yi wajen ganin sun taimaka masu don gudanar da aikin su.

A wani labarin kuma, Wani mutum mai suna Toni Iwobi wanda dan asalin kasar Najeriya ne da aka haifa a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya ya samu nasarar zama dan majalisar dattijai a kasar Italiya dake tarayyar turai a zaben da ya gudana.

Shi dai Mista Iwobi kamar yadda muka samu ya tafi kasar ta Italiya ne tun shekara ta 1970 inda kuma ya shiga harkar siyasar kasar kafin daga bisani ya samu mukamin jami'in 'yan kasar waje na jam'iyyar sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel