Nigerian news All categories All tags
Za a fara amfani da yaren uwa wajen koyar da yara a makarantun firamare

Za a fara amfani da yaren uwa wajen koyar da yara a makarantun firamare

- Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar fara koyar da yara a makarantun firamare da yaren iyayensu

- Ministan ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana hakan yayin halartar wani taro jiya a Abuja

- Darekta a bankin duniya, Rachid Bennessaoud, ya yi alkawarin hada karfi da gwamnatin tarayya domin inganta harkar koyo da koyarwa

Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar fara koyar da yara a makarantun firamare da yaren iyayensu. Za a ke amfani da yaren uwa wajen koyar da yaran da basu wuce aji uku a firamare ba.

Ministan ilimi Adamu Adamu ya bayyana haka jiya a Abuja yayin halartar wani taron rahoto a kan cigaban ilimi da bankin duniya ta dauki nauyi.

Za a fara amfani da yaren uwa wajen koyar da yara a makarantun firamare

Adamu Adamu

Ministan na yin wadannan kalamai ne a matsayin martani ga tambayar da aka yi masa a kan koyar da yara cikin harshen iyayen su domin saukaka koyo da koyarwa.

DUBA WANNAN: Magu ne mafi cancanta ya rike EFCC – Osinbajo

Darekta a bankin duniya Rachid Bennessaoud ya bayyana cewar harkar koyo da koyarwa ta wuce maganar inganta ajuzuwan daukan darasi tare da yin alkawarin hada karfi da gwamnatin tarayya domin inganta harkar ilimi.

Wasu masu nazarin harkar ilimi a kasar nan na ganin cewar tabarbarewar ilimi na da alaka da koyar da yara da yaren da ba na su ba kuma ba su da fahimtar sa a matakin koyo na farko.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel